Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnan Kano Abba Gida-Gida ya ƙaddamar da Auren Gata na mutane 3600

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da Auren Gata da akafi sani da auren Zawarawa a yau juma’a 13 Oktoba shekarar 2023

A ranar Juma’a ne gwamnatin jihar Kano ta gudanar da daurin auren maza da mata 3,600 a fadin kananan hukumomin jihar 44

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ƙaddamar da daure An daura auren ne a fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Bayero a yau

Wadanda suka ci gajiyar tallafin sun haɗar da ‘yan mata da maza, zawarawa, wadanda suka rasa mazan su kuma sun fito ne daga kananan hukumomi 44 na jihar

Bikin ya samu halartar Gwamna Abba Yusuf Jagoran Kwankwasiyya, Dr Rabiu Kwankwaso, jami’an gwamnati da malaman addini Alhaji Yusuf Nabahani Madakin Kano ne ya wakilci Sarkin Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa za’ayi walimar auren domin inganta al’adu da da kuma taya su murna kan yadda suka angwance

Ya sanar da cewa, za a ci gaba da gudanar da bukukuwan a ranar Asabar da tare da walima a gidan gwamnatin Jihar

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!