Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnan kano ya bada umarnin rufe duk wani asusu na ma’aikatu da hukumomin gwamnati

Published

on

Gwamnatin kano ta bada umarnin kwanaki 7 domin rufe duk wasu asusun ma’aikatu da hukumomin gwamnati dan aiwatar da tsarin asusun bai ɗaya domin daƙile cin hanci a hukumomin da ma’aikatun mallakin gwamnatin jihar.

Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne yayi wannan jawabin a yau yayin taron masu ruwa da tsaki kan aiwatar da tsarin asusun bai ɗaya da haɓɓaka kuɗaɗen shigowa a faɗin kano.

Gwamnan ya tabbatar da cewa wannan matakin ya biyo bayan yadda ake samin zirarewar kuɗi a ma’aikatu da hukumomin gwamnati da yadda ake ƙara samin raguwar kuɗaɗen shiga na jihar.

Da yake jawabi shugaban hukumar tattara haraji na jihar Kano Alhaji Zaid Abubakar ya tabbatar da cewa wannan tsari da gwamnatin kano tayi zai taimaka wajen tara haraji da yadda za’a magance zirarewar kuɗaɗen gwamnati.

Haka zalika gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci dukkannin shugabannin ma’aikatun gwamnatin da zamo masu bayar da haɗin kai wajan aiwatar da wannan tsarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!