Labarai
Gwamnan Kano ya shawarci ‘yan Fansho suyi amfani da kudin da aka basu ta hanyar da ta dace

Gwamnan jihar kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga dukkanin waɗanda suka karɓi kuɗin hakkinsu na garatuti da su kasance masu mayar da hankali wajen amfani da abin da suka samu ta hanyar da ta dace domin amfanin kansu da iyalansu.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron bayar da kuɗin garatuti ga ƴan fansho karo na biyar na adadin kudi naira biliyan biyar da ya gudana a fadar gwamnatin Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya ce manufar wannan shiri shi ne taimaka wa tsoffin ma’aikata waɗan da suka kammala aiki domin su samu walwala da kuma rayuwa mai nagarta bayan kammala hidimtawa jiharsu.
Ya kara da cewa gwamnati tana da niyyar ci gaba da biyan dukkanin masu hakkinsu a matakai daban-daban har sai an tabbatar da kowa ya samu nasa tare da jan hankalin masu karɓa da su guji amfani da kuɗin ta hanyoyin da ba su da amfani.
Haka zalika Gwamnan ya shawarci tsoffin ma’aikatan da su yi amfani da kuɗin wajen sana’o’in dogaro da kai da zuba jari domin kare kansu daga dogaro da wasu domin hakan zai ba su damar ci gaba da gudanar da rayuwa mai inganci.
You must be logged in to post a comment Login