Labarai
Gwamnan Kano Ya taya murnar Sabuwar Shekarar 2024
An yi farin ciki yayin da Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf tare da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo da sauran manyan jami’an gwamnati suka gabatar da sabuwar shekara ta 2024 da dimbin jama’a suka halarta a harabar Mahaha Sport.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa da ya fitar ya kuma rabawa manema labarai.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce dole ne shekarar 2023 ta cika ganin yadda al’ummar Kano suka zabi jam’iyyar NNPP domin gudanar da al’amuran jihar tare da amincewa da gudunmawar matasa da mata a lokacin zabe.
Gwamnan ya ce shekara ta 2024 za ta kasance da manya-manyan ayyuka na ci gaban al’umma waɗanda ke da alaka kai tsaye ga rayuwar al’ummar jihar tare da kudurin yada ribar dimokuradiyya a cikin lungu da sako na Kano.
Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta kammala gine-gine a filin wasanni na Mahaha don zama cibiyar nishadantarwa, tarukan jama’a da na addini baya ga harkokin wasanni wanda shi ne babban abin da ya fi daukar hankali a rukunin.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kwarin gwiwar sa wajen aiwatar da ayyukan wasanni domin hada kan matasan jihar da sauran bangarori domin bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin jihar.
Ya kuma yabawa al’ummar jihar bisa goyon baya da hadin kan da suke baiwa gwamnatin sa tare da fatan dorewar nasara domin kai jihar ga wani matsayi mai girma.
You must be logged in to post a comment Login