Labarai
Gwamnan Kano ya umarci a gaggauta yanke hukunci kan wadanda suka kashe iyalai 7

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci Kwamishinan Shari’a na jihar da a gaggauta ɗaukar matakin shari’a kan duk waɗanda ake zargi da hannu a kisan mata da ’ya’yanta shida a unguwar Dorayi da ke cikin birnin Kano.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa iyalai da kuma mijin marigayiyar, inda ya nuna matuƙar alhini da jimami kan wannan mummunan lamari da ya girgiza al’ummar jihar.
Gwamnan Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci duk wani nau’in tashin hankali ko kisan gilla ba, tare da jaddada aniyar gwamnati na tabbatar da adalci ta hanyar hukunta duk masu hannu a aikata wannan aika-aika.
kazalika ya kuma jajanta wa iyalan mamatan tare da addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya kuma bai wa waɗanda abin ya shafa haƙurin jure wannan babban rashi.
haka kuma ya tabbatar wa al’ummar Dorayi da daukacin jama’ar jihar Kano cewa gwamnati na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login