Labarai
Gwamnan Kano ya ware Naira Biliyan Biyar domin biyan ƴan fansho
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da sake biyan waɗan sa suka yi ritaya ƙarin kuɗi naira biliyan biyar domin raba kashi na biyu na kudin fansho ga ma’aikatan da suka yi ritaya a jihar.
Wannan na ƙunshe ta cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yau a yayin da aka fara taron majalisar zartarwa ta jihar Kano karo na goma sha hudu da ya gudana a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin Kano.
Idan dai ba a manta ba a shekarar da ta gabata ne gwamnatin kasar ta fitar da naira biliyan shida domin biyan dubban ƴan fansho da ba su samu hakkokinsu ba a tsawon shekaru takwas na gwamnatin da ta shude.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa an biya wadannan kudade ne domin tallafa wa wadanda suka yi ritaya da kuma sanya farin ciki a rayuwarsu, domin da yawa sun dau shekaru suna jiran ba tare da samun hakkokinsu ba duk da sadaukarwar da suka yi wa jihar a tsawon shekarun aiki.
“Mun himmatu wajen tabbatar da jin dadin ma’aikatan gwamnati da wadanda suka yi ritaya a jihar,” in ji Gwamnan.
Gwamna Yusuf ya kuma tattauna kan shirye-shiryen share magudanun ruwa a cikin birnin Kano domin ƙaratowar lokacin damina, ya kuma umurci jami’an riko na kananan hukumomi da su yi shiri wajen magance matsalar.
An kafa wani kwamiti mai karfi wanda Mataimakin Gwamna ya jagoranta, domin sa ido kan yadda za’a magance matsalar lalacewar magudanun ruwa a dukkan kananan hukumomi 44, domin hana aukuwar ambaliyar ruwa a lokacin damina.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su yi hakuri domin gwamnati ta yi namijin kokari wajen ganin ta magance matsalolin karancin ruwa a Kano duk da matsalolin injina da rashin samar da wutar lantarki da ke kawo cikas ga gudanar da ayyukan hukumar ruwa ta jihar.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana jin dadinsa ga al’ummar jihar bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnatinsa tare da ba su tabbacin cika alkawuran da ya dauka a yakin neman zabe domin bunkasa ci gaban jihar Kano.
Bugu da kari kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya ba gwamnan lambar yabo da kungiyar kwararrun ma’aikatan lafiya ta kasa (NACPHPN) ta baiwa gwamnan bisa kokarinsa na inganta fannin.
You must be logged in to post a comment Login