Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnan Kano yayi alƙawarin bayar da tallafi ga ma’aikatan gidan Gwamnati

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kafa tarin a gidan Gwamnatin Kano inda jagoranci shan ruwa da ɗaukacin ma’aikatan fadar gwamnatin Kano da suka haɗar da manyan Daraktoci da sauran bangarori da suke aiki a gidan Gwamnatin.

Shan ruwan ya biyo bayan irin ƙoƙarin da ma’aikatan cikin gidan suke yi wajen gudanar da ayyukan jihar.

Wannan na ƙunshe ta cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Babban Daraktan yaɗa labaran Gwamna Sunusi Bature Dawakin Tofa da ya fitar a ranar Lahadi.

Da yake jawabi Gwamna Yusuf ya bayyana ƙoƙari da irin rawar da ma’aikatan cikin gidan Gwamnati suke bayarwa a kullum wajen gudanar da ayyukan gwamnati, adan haka ya zama dole mu yaba muku kuma mu samar muku hanyoyin da zamu taimake ku.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kuma ce yanzu haka a tsarin sa akwai tsarin bayar da tallafi ga ma’aikatan gidan Gwamnati da sauran ma’aikatan gwamnati da suke jihar.

Daga ƙarshe gwamnan ya yabawa dukkanin ma’aikatan faɗar gwamnatin Kano dama al’ummar jihar baƙi ɗaya inda ya sha alwashin ci gaba da fito da tsare-tsaren da zasu ciyar da kano gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!