Labarai
Gwamnan Lagos ya kaddamar da yin rijistar Jarirai

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya kaddamar da tsarin rajistar jarirai ta hanyar amfani da fasahar zamani da kuma tsarin rajistar yara daga wata daya zuwa wata goma sha biyu ta hanyar na’ura.
Gwamnan ya bayyana wannan shirin a matsayin muhimmin mataki da zai taimaka wajen samun sahihin bayanai a kai a kai domin ingantaccen tsarin mulki da cigaban jihar.
Sanwo-Olu ya ce wannan tsarin zai taimaka wajen sauƙaƙa samun bayanai game da yara da kuma tabbatar da cewa babu wanda aka bari a baya wajen cin gajiyar shirye-shiryen kewon lafiya a jihar.
You must be logged in to post a comment Login