ilimi
Gwamnati Sokoto ta gargaɗi shugabannin Makarantun Sakandire

Gwamnatin jihar Sokoto ta gargaɗi Shugabannin Makarantun Sakandire kan su guji karɓar ƙudi a hannun ɗalibai da sunan kuɗin jarrabawa.
Wanann na cikin sanarwar da Kwamishinan Ilimi na jihar Farfesa Ahmad Ladan Ala ya fitar.
Sanarwar ta ce, maʼaikatar ilimi ta samu ƙorafe-ƙorafe cewa wasu ʼPrincipalsʼ na karɓar kuɗaɗe daga wajen ɗalibai kafin basu damar rubuta jarrabawa.
Ya ce, wannan babban laifi ne, domin gwamnan jihar ya riga ya biya dukkan waɗannan kuɗaɗe.
Sanarwar ta buƙaci iyaye da ɗalibai su kai rahoton duk makarantar da aka bukaci su bada kuɗi.
You must be logged in to post a comment Login