Labarai
Gwamnati ta amince da a fara kawo motoci don maye gurbin masu adaidaita
Gwamnatin jihar Kano ta yi ƙarin haske kan shirin ta na kawo motocin sufuri da za su maye gurbin matuƙa baburan adaidaita sahu.
A zantawar sa da Freedom Radio Kwamishinan Sufuri da Gidaje na jihar Kano Malam Mahmud Muhammad Santsi ya ce, dama tuni Gwamnatin Kano ta yi tsari domin tsaftace zirga-zirga a jihar.
Kwamishinan ya ce, sakamakon zanga-zangar masu adaidaita sahu, Gwamnati ta bai wa kamfanin zirga-zirga na jihar wato Kano Line umarnin ya sako motoci su bi titi domin su sauƙaƙa wa al’umma sufuri.
Sannan akwai wani kamfani da tuni ya fara tattauna wa da Gwamnati a baya kan kawo motocin sufuri a Kano.
A cewar Kwamishinan tuni ya baiwa kamfanin Kano Line da kuma wani sabon kamfanin da ke neman sahalewar gwamnatin Kano don fara sufuri damar sako motocin su kan titi don daukar jama’a.
Mahmud Santsi, ya kuma nemi jama’ar Kano da su kwantar da hankulan su, domin Gwamnati tana tare da su, kuma tana yin dukkan waɗannan tsare-tsare ne domin jin daɗin su a cewarsa.
You must be logged in to post a comment Login