Manyan Labarai
Gwamnatin Buhari na bin umarnin Kotu- Abubakar Malami
Ministan shari’a kuma Antoni Janar na Nigeria Abubakar Malami ya musanta zargin da al’umma ke yi akan gwamnatin tarayya na bijirewa umarnin kotu akan sakin mutane uku da kotu ta ba da belinsu, Kanar Sambo Dasuki da Malam Ibrahim Zakzaki da kuma Dan jarida Omoyele Sowore.
Abubakar Malami ya bayyana hakanne a zantawarsa da shirin Kowanne Gauta na Freedom Radio.
Yana mai cewa, duk wani umarnin kotu da gwamnatin tarayya ta bijirewa ta na da hujja a dokar kasa na kin bin umarnin kotu da aiwatar da shi da gaggawa.
Ya kara da cewa, a tsarin dokokin Nigeria mutum na da damar kalubalantar umarnin dan kotu ta baiwa mutum na yin wani abu, kuma ya na da damar kin yin abinda kotun ta umarce shi ko kuma ya nemi kotu ta canja umarni da ta yi ko ta ba da damar daukaka ka.
Aubakar Malami yace, dukkan kararrakin da ake zargin gwamnatin tarayya ta ki bin umarnin kotu duk suna matakin Hight Court ne, babu karar da ta ke a kotun koli.