Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Gwamnatin jahar Kaduna ta bukaci a kau da Almajiranci

Published

on

Kwamishiniyar cigaban alumma ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba tayi kira ga jihohin Arewacin kasar nan sha tara 19 da su samar da manufofi da tsare-tsare mai kyau wajen cimma nasarorin kauda karatun Almajiranci a yankin.

Hajiya Hafsat Baba tayi wannan kiran ne yayin da take kare kunshin kasafin kudin ma’aikatar ta ,a gaban  kwamitin kula da bunkasa al’umma na majalisar dokoki ta jihar.

Kwamishiniyar ta nunar cewar, kafin a kauda Almajirai akan tituna kamata yayi a samar da tsare-tsaren da suka dace wajen shawo kan matsalar.

“Ta ce nauyin ya rataya a wuyan dukkanin jihohin Arewacin kasar nan sha tara 19 ta yadda za su samar da manufofi da za su warware matsalar acewar Hajiya Hafsat “

Har ‘ila yau Kwamishiniyar ta ce almajiran da ma’aikatar ta kawar akan titinan jihar ta Kaduna sun gano cewar sun fito ne daga jihohin Arewacin kasar nan suka fito.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!