Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Jami’ar Bayero ta kama dalibai shida da zargin magudin jarrabawa.

Published

on

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Bayero,  sashen  tsangayar kimiyya da fasaha, ta gayyaci daliban tsangayar su shida  bisa zargin su da aikata magudin jarrabawa.

Malamin da ke kula da shiryawa da rubuta jarrabawa na sashen nazarin kimiyyar na’ura mai Kwakwalwa, Sa’ud Adam Abdulkadir, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa  dauke da sa hannun sa.

Malam Sa’ud Adam Abdulkadir, ya ce ana zargin daliban da aikata magudin jarrabawa da kuma samun takardar tambayoyin jarrabawa kafin ranar da za’a gudanar da jarrabawar.

Ya ce  daliban za su bayyana a gaban kwamitin kula da rubuta jarrabawa na tsangayar ranar Litinin 11 ga watan Nuwambar da muke ciki domin kare kansu a kan zargin da a keyi musu.

Wakilin mu Anas Muhammad Mande, ya ruwaito ce wa an kama daliban yayin da a ke gudanar da jarabawar karshen zangon shekarar 2018/2019.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!