Labarai
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin tudun mun tsira ga waɗan da suka tuba daga harkar daba

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da shirin tudun mun tsira ga dukkanin waɗan da suka tuba daga harkar daba a faɗin jihar kano domin tabbatar da an tsaftace jihar daga duk wani tashe tashen hankali da yake da nasaba da harkar faɗan daba da sace-sace.
Gwamnan jihar kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya ƙaddamar da shirin a yau domin tattaunawa da dukkanin shugabannin waɗan da suka ajiye makaman su daga harkar daba, domin kare jihar kano daga dukkanin wani tashe tashen hankula da suke addabar jihar.
Gwamnan Abba Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kwamrat Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce Gwamnatin kano ta gama shiri tsaf ƙarƙashin hukumar ƴan sanda ta jihar wajen tantance dukkan wadan da suka tuba ta yadda za’a samar musu da aikin yi.
You must be logged in to post a comment Login