Labarai
Gwamnatin Kano na shirin daukar mataki kan yan Achaba

Gwamnatin jihar Kano, ta ce, za ta hukunta duk wani da aka samu na amfani da tukin babur mai kafa biyu da sunan yin sana’ar Achaba, wanda tace da ma can yinta haramun ne.
Mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin Sufuri Danladi Idris Karfi ne ya bayyana hakan, bayan samun rahotonni kan yadda wasu bata gari ke ci gaba da gudanar sana’ar a wasu sassan birnin Kano, wadda gwamnati ta haramta tun a shekarun baya.
Danladi Idris Karfi, ya ce, tun a baya gwamnatin Kano ta haramta gudanar da sana’ar babur mai kafa biyu, kuma gwamnati a yanzu karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ba zata lamunci barin wasu ci gaba da gudanar da ita ba.
Ya kuma ce duk wanda aka sake samu da aikata wannan sana’a ta achaba a birnin Kano, da kewaye, babbu shakka zai fuskanci hukuncin da doka ta tanadarwa wanda ya aikata hakan.
A baya bayannan dai anga yadda sana’ar tukin babur mai kafa biyu ke ci gaba da yawaita a kwaryar birnin Kano da kewaye, wanda Gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ce za ta ci gaba da bakin kokarinta domin magance matsalar tsaro a wasu sassan jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login