Labarai
Gwamnatin Kano na shirin horar da matasa miliyan 1.5 a fannin fasahar zamani

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirin horar da matasa miliyan 1.5 a fannin ilimin fasahar zamani da ƙwarewar zamani domin rage zaman kashe wando da bunƙasa tattalin arziki.
Shugaban Hukumar Ci gaban Fasahar Sadarwa ta Jihar Kano KASITDA, Dakta Bashir Abdu Muzakkari, ya ce, shirin Kano State Digital Economic Policy and Digital Transformation Agenda zai gudana daga shekarar 2025 zuwa 2027, tare da raba matasan zuwa matakin asali, matsakaici da na ƙwararru.
Ya ce matasa 150,000 aka fara ɗauka a matsayin shirin gwaji, yayin da fiye da 1,100 suka kammala karatu daga cibiyoyin horo na jihar.
Haka kuma, an ƙaddamar da shirin Hackathon HEAT (Health, Education, Agriculture and Transportation) domin ƙirƙirar mafita da samar da ayyukan yi ga matasa.
Ƙungiyar KALM Community Initiative, wacce ke haɗin gwiwa da KASITDA, ta ce manufarta ita ce buɗe ƙofofi ga matasa a fannin fasahar zamani, tare da saukar da shirin zuwa ƙananan hukumomi da sauran sassan ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login