Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masu Murnar cin Zabe ne suka lalata fitulun Titina- Gwamnatin Kano

Published

on

Yayin da tituna ke ci gaba da kasancewa cikin duhu musamman cikin dare a jihar Kano, Hukumar Ƙawata Birnin jihar ta ce, wasu ɓata-gari ne suka lalata Fitilun yayin gudanar da murnar lashe zaɓen Gwamna, lamarin da ya sanya yanzu ba a kunna fitilun.

Hukumar ta kuma ce matsalar na da alaka kuma da batun matsalar tsadar Man Deisel da kuma wahalarsa.

Malam Usman Datti Abdullahi shi ne mai magana da yawun hukumar, ya kuma kara da cewa, wannan matsalar ta samo asali ne tun bayan da masu murnar cin zabe suka lalata wasu daga cikin wayoyin da ke bada hasken wutar lantarki a bangarori da dama na kwaryar birnin Kano’.

‘Haka zalika tsada disa, da kuma karancinsa ya taka rawa wajen kawo karancin wutar lantarki a Jihar Kanon,wanda ya ce da kudin su ma a wasu lokutan basa iya samun dizal din,wanda ya ke sanyawa dole a wannan lokacin a hakura da bada wutar lantarkin’.

Malam Usman Datti Abdullahi ya kara da cewa, hukumar dukufa wajen kawo karshen matsalar a fadin Jihar Kano.

Rahoton: Hafsat Abdullahi ‘Danladi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!