Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta bada aikin magance zaizayar kasa a Gayawa da Bulbula kan fiye da Biliyan 8

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta bayar da kwangilar aikin magance matsalar zaizayar kasa a yankunan Gayawa da Bulbula a kan kudi Naira Miliyan dubu takwas da dari hudu da casa’in da bakwai da dari biyar da casa’in da biyar da naira dari biyu da casa’in.

Da ya ke mika takardar aikin kwangilar jiya Laraba ga kamfanin da zai gudanar da aikin, kwamishinan Muhalli da kare matsalolin sauyin yanaki na Kano Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya ce, gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da aikin ne karkashin shirin dakile matsalar kamfar ruwa da matsalolin sauyin yanayi a wuraren tsandauri watau ACReSAL.

Kwamishinan, ya kara da cewa, wannan aiki zai taimaka matuka waje kare sake afkuwar irin wannan matsala ta zaizayar kasa a yankunan.

Haka kuma ya ce ‘’ Ina mika sakon godiya ta ga mai girma gwaman Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa sahale yin wannan aiki wanda mun jima muna so a yi shi tun ma a lokacin shirin New Map, sai ga shi yanzu cikin ikon Allah an bayar da wannan kwangila.’’

Kwamishinan, ya kuma ce, ‘’ Ina kara godiya ga mazauna wadannan yankuna bisa gudunmawar da suka bau wajen ganin an gudanad da wannan aiki, kuma tuni mai girma gwamna ya sahale a sayi gidajensu da ke wurin da aka samu wannan matsala za a biya su har fiye da Naira miliyan ɗari shida don su tashi daga wurin da za a fara gudanar da wannan aiki.’’ 

A nasa bangaren, guda cikin jagororin kamfanin da zai yi aikin Injiniya Ammar Nureen, ya bayyana cewa, suna da kwarin gwiwar kammala aikin a kan lokacin da suka diba kuma zai kasance mai inganci kamar yadda suka yi irinsa a wasu daga cikin jihohin Arewacin kasar nan.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!