Labarai
Gwamnatin kano ta bayar da tallafi ga iyalan ɗan Vigilanten da ya rasa ran sa
Gwamnatin jihar Kano ta bayar da tallafin kayan abinci da kuɗi ga iyalan wasu ƴan Vigilante da suka rasa ransu da wa’inda suka jikkata yayin gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jihar Kano, inda ake zargin wasu ɓata gari da aiwatar da hakan
Da yake bayar da tallafin ga iyalan mamacin da wa’inda suka jikkata Babban Daraktan Ayyuka na musamman AVM Ibrahim Umar me murabus ya bayyana damuwarsa bisa yadda wasu ɓata gari sukayi anfani da wannan damar wajen jikkata al’umma.
AVM mai murabus ya ce gwamnatin jihar kano na mutuƙar yabawa da irin aikin da ƴan sa kai na Vigilante sukeyi a faɗin jihar kano domin bayar da tsaro a lungu da saƙo na jihar adan haka ya zama wajibi gwamnati ta taimaka musu.
Malan Auwalu Idris Mai kankana Mahaifi ne ga ɗaya daga cikin Ƴan Vigilanten da ya rasa ransa yayi mana ƙarin haske kan irin halin da suka shiga sakamakon rashin na shi.
Inda yace wannan mamacin ya rasu yabar mata ɗaya da yara huɗu, kuma yanzu haka basu da mahallin zama nasu nakan su, inda a yanzu ba su da yadda zasuyi shiyasa suke kira ga gwamnatin kano da ta tallafa musu domin rashin ɗan nan nasu basu da yadda za’suyi.
Yunusa Ibrahim Yunusa shima ɗaya daga cikin wa’inda suka jikkata a wannan lokaci ya ce yana matuƙar godiya ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf bisa yadda akayi duba da irin halin da ya shiga wajen bayar da tallafin kayan abinci gare shi da kuɗaɗe wannan ba ƙarin karamci bane.
Kuma zamu ci gaba da bayar da gudummawa ga al’ummar jihar Kano musamman wajen bayar da tsaro a cikin lungu da saƙo dake faɗin jihar kano domin tabbatar da an samar da tsaro me ɗorewa. A cewar yunus.
Haka kuma Babban Daraktan Ayyuka na Musamman AVM Ibrahim Umaru mai murabus ya sha alwashin miƙa buƙatun iyalan mamacin ga gwamnan jihar Kano domin tabbatar da an taimake su
A yayin bayar da tallafin an bawa matar mamacin kuɗi naira dubu ɗari biyar da manyan bohun sinkafa guda biyu sai kuma lambar girmamawa inda kuma aka bawa mahaifan mamacin dubu ɗari.
Shima Yunusa da jikkata an bashi babban buhun Sinkafi da kuɗi narai dubu hamsin da kuma lambar yabo ta girmamawa da kuma ƙarin girma
You must be logged in to post a comment Login