Labarai
Gwamnatin Abba Kabir ta dakatar da albashin sabbin ma’aikatan da Ganduje ya dauka
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da biyan albashin ma’aikata Dubu 10 da Dari 8 daga wannan watana Yuni, har sai an kammala binciken bisa zargin daukarsu aiki ba bisa ka’ida ba.
Babban Akanta na Jihar Abdulkadir Abdusalam, ne ya bayyana hakan, yayin da ya ke yi wa Freedom Radio karin haske akan dalilan da ya sanya suka tsayar da albashin ma’aikatan.
Ya ce, akwai zargimai karfi na cewa gwamnatin da ta gabata ta dauki ma’aikatan ne ba bisa ka’ida ba.
Abdusalam ya kuma ce, dukkanin ma’aikata da suka hadar da na kananan hukumomin da aka kwaso ba bisa ka’ida ba aka mayar da su wasu ma’aikatun gwamnati domin samun albashi mai tsoka, a wannan wata zasu biyasu abashinsu na asali da aka dauke su aiki.
Babban Akantan na Kano ya kuma ce, kowanne lokaci daga yanzu ma’aikatan Kano da ‘Yan fansho za su fara samun albashinsu haka ma yan fanshon za su samu hakkinsu na wannan wata.
You must be logged in to post a comment Login