Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu sake gina shataletalen gidan gwamnati a Na’ibawa- Abba Kabir

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta sake gina shataletalen kofar gidan gwamnati da ta rushe a gadar shigowa gari da ta ke a unguwar Na’ibawa.

Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, ne ya bada umarnin rushe shataetalen da ke kofar fadar gwamnatin jihar a baya, saboda dalilan tsaro tare da kudirta sake gina shi a wajen da ya dace.

Mukaddashin Sakataren yada Labaran gwamnan jihar Hisham Habib, ne ya sanar da hakan, ta cikin sanarwar da ya fitar a daren Lahadin nan.

Ya ce, Gwamna Abba ya gana da Kaltume Ana wadda ta yi zanen shataletalen mai dauke da alamar cikar Kano shekaru 50 da kafuwa, tare da cimma matsayar sake gina sabon shataletalen mai inganci domin kara kawata Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!