Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin Kano ta fara feshin maganin cutar Covid-19

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce nan ba da jimawa ba za’a fara feshin maganin kashe kwayoyin cuta a Masallatai da Kasuwannin jihar Kano, inda ta ce dole ce ta sanya aka rufe hanyoyin shigowa jihar Kano ba wai son rai ba, kasancewar hakan na cikin hakan na cikin manyan hanyoyin hana shigowar cutar Covid-19 cikin kasar nan.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba ne ya bayyana hakan jim kadan bayan shirin barka na nan freedom radiyo wanda mayar da hankali kan yadda gwamnati ta bada dokar rufe hanyoyin shigowa jihar nan da dokar zata fara aiki da misalign 12 na daren yau.

Kwamishinan ya kuma kara da cewar, rufe iyakokin jihar nan ne kadai hanyar da za’a bi wajen hana shigowar cutar Corona kasancewar cudanya da juna na cikin manyan hanyoyin kamuwa da ita.

A nasa bangaran kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Kabiru Ibrahim Tsanyawa ya bayyana cewar gwamnatin tana gudanar da aikin Gyaran cibiyar kula da marasa lafiya ta ‘yar Gaya tare da kara inganta wasu daga cikin asibitici da kuma sanya kayayyakin kula da lafiyar a wani bangare na shirin ko ta kwana don yaki da cutar.

Kabiru Ibrahim Tsanyawa ya kuma bukaci al’umma da su kasance masu kula da tsaftar muhalin su tare da bin dokar da gwamnati ta gindaya, tare da bin shawarwarin likitoci da kuma kaucewa shiga cinkoson jama’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!