Labarai
Gwamnatin Kano ta fara kwato motocin da wasu tsoffin kwamishinoni suka tafi da su

Gwamnatin Jihar Kano ta fara kwato motoci mallakin gwamnati da wasu tsofaffin kwamishinoni suka tafi da su bayan yin murabus din su.
Shugaban Hukumar karbar korafi da yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Comrade Sa’idu Yahaya ne ya jagoranci aikin a yau Alhamis.
Ya ce ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ya rubuta wasiku ga tsofaffin jami’an domin su mayar da motocin, amma suka gaza bin umarnin, lamarin da ya sa aka dauki matakin kwato su.
Daga cikin wadanda aka kwato motocin hannun su akwai tsohon Kwamishinan Tsaro, Air Vice Marshal Ibrahim Umar da tsohon Kwamishinan Matasa, Mustapha Rabiu Kwankwaso sai tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata da tsohon Kwamishinan Jin Kai Dakta Adamu Aliyu Kibiya, da tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Nasiru Sule Garo.
Hukumar ta ce, za ta ci gaba da daukar matakai domin kare dukiyar gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login