Labarai
Gwamnatin Kano ta gamsu da aiyyukan Titin Kilomita 5 na Ajingi, Wudil da Takai

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana gamsuwar ta ga aiyyukan Titin Kilomita biyar dake gudana a kananan hukumomin Ajingi, Wudil da Takai da a baya al’ummar yankin suka yi fama da kalubalen hanyoyin.
Aikin titin Kilomita biyar na Ajingi wanda ya lakume sama da Biliyan uku a baya yana da ga cikin da aka kwace daga hannun dan kwangilar da ya fara shi sakamakon tsaikon da ake samu, kafin sake bayar da shi ga wani sabon dan kwangilar da ya ke ci gaba da aiwatar da shi bayan korafin da al’ummar a yankin suka yi.
Da yake jawabi ga kwamishina da ‘yan tawagar ma’aikatar bibiya da lura da aiyyukan gwamnatin jihar Kano, daya daga cikin shugabannin al’ummar yankin na Ajingi, Alhaji Shehu Isa Ajingi, bayyana yadda aikin ke gudana ta re da yabawa gwamnatin jihar.
A nasa jawabin kwamishinan ma’aikatar Kwamred Nura Iro Ma’aji Sumaila, ya ce aiyyukan suna ci gaa da tafiya yadda ya kamata kuma za a kammala su a cikin watan Disamba kamar yadda gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya sa wa’adin kammalawa.
A lokacin ziyarar duba aiyyukan kwamishina Nura Iro Ma’aji Sumaila, tare da tawagar ma’aikatar sun duba aikin ginin Masallacin Jumma’a na Rijiyar Gwangwan, dake Jido, a karamar hukumar Dawakin Kudu, da wasu sauran aiyyukan da ake gudanarwa wadan da ke dab da kammaluwa.
You must be logged in to post a comment Login