Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta musanta karbar takardun masu neman tallafin karo karatu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta karyata jita-jitar cewa ta fara karɓar takardun masu neman tallafin karatu zuwa ƙasashen waje da cikin gida karkashin shirin “1001 scholarship program”.

 

Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban hukumar tallafin karatu ta jihar Kano Kabiru Getso Haruna, ya fitar a ranar daren jiya Lahadi.

 

Sanarwar ta bayyana cewa wasu na kiran mutane da cewa sun samu gurbin tallafi daga hukumar, tare da neman su tura takardunsu zuwa Abuja don neman visa da tabbatar da takardu, abin da hukumar ta ce ba gaskiya ba ne.

 

Hukumar ta shawarci jama’a da su yi hattara da irin wadannan sakonni ko kira, sannan su tabbatar da duk wani bayani daga sahihin tushe na hukumar, kuma su guji aika muhimman takardunsu ga mutanen da ba su sani ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!