Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Gwamnatin Kano ta rufe asibiti mai zaman kan sa a Gaya

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wani asibiti mai zaman kan sa a ƙaramar hukumar Gaya.

An rufe asibitin bisa laifin ɗaukar wasu masana a fannin ilimin abinci mai gina jiki a matsayin malaman jinya.

Sakataren zartarwa na hukumar kula da asibitoci masu zaman kansu PHIMA Dakta Usman Tijjani Aliyu ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.

Ya ce “Asibitin Nasaha da ke karamar hukumar Gaya, an rufe shi ne bisa laifin mika wasu marasa lafiya zuwa ga masanin abinci mai gina jiki a matsayin ya basu kulawar da ta dace, baya ga laifin rashin tsafta da aka gano a asibitin”.

Dakta Tijjani ya ce, bisa korafin da jama’ar yankin ke yin a rashin samun kulawar da ta dace a asibitin. ya sanya aka aike da jami’ai don yin bincike kuma aka kama su da laifi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!