Labarai
Gwamnatin Kano ta sha alwashin karfafa dokokin kare mata daga cin zarafi
Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin yin tsayin daka wajen samarwa mata sana’o’in dogaro da kai tare da karfafa dokokin kare mata daga cin zarafi.
Kwamishiniyar ma’aikatar kula da harkokin mata da walwalar kananan yara ta Jihar Kano Dakta Zahra’u Muhammad Umar ce ta bayyana haka yayin bikin tunawa da ranar mata ta duniya da aka gudanar jiya Litinin 8 ga watan Maris din 2021 a fadar gwamnatin Kano.
Dakta Zahra’u Muhammad Umar ta ce ma’aikatar ta ta za ta fito da dabarun koyawa mata sana’o’in ne domin dogara da kai, tare da rage radadin da wasunsu ke fuskanta na cin zarafi daga mazajensu.
“Hakan ya zama wajibi la’akari da matsayin mata na iyayen al’umma da ke kula da tarbiyyar ‘ya’ya tun daga gida,” inji Dakta Zahra’u.
A na ta bangaren a yayin taron, maidakin gwamanan Kano Hajiya Hafsat Abdullahi Ganduje, ta ce mata sun cancanci duk wata kulawa ta duniya kasancewar ginshikin ci gaban rayuwar al’umma.
Kafin karkare taron, kungiyoyi masu zaman kansu sun yi rabon kyautuka ga mata.
Taken bikin na bana shi ne: Mata A Shirye Suke Su Fuskanci Kalubalen Dake Gabansu.
You must be logged in to post a comment Login