Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rahoton wasu cikin kalubalen da mata da kananan yara suka fuskanta a 2022

Published

on

Shekarar da muka yi ban kwana da ita ta 2022, mata da kananan yara sun fuskanci kalubale iri-iri na rayuwa a fadin duniya na cin zarafi da muzgunawa, wanda hakan ke ci gaba da tagayyara rayuwarsu.

Kalaubalen ya hada da fyade ko musgunawa daga wasu makusantansu, rashin damawa da su a harkokin shugabanci, wanda ke jefa rayuwarsu cikin kunci.

Wani rahoto da asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya fitar a baya-bayan nan, ya nuna cewa akalla mace guda a cikin mata hudu a Najeriya kan fuskanci cin zarafin fyade kafin cika shekaru goma sha takwas da haihuwa, daidai da kashi 42 da digo 3 cikin dari kenan.
A cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, a Najeriya an samu karuwar matsalar fyade da kuma rashin yi wa matan da aka yi wa fyaden adalci, ko da kuwa sun yi kokarin shigar da kara a gaban kotu.
Amnesty ta ce akwai daruruwan matan da aka yi wa fyade da ba a san takaimaimen yawansu ba, saboda da dama daga cikinsu sun gwammace su rufe bakinsu don gudun tsangwama ko kuma kyamata.
A jihar Adamawa, mata da kananan yara 363 ne aka yi wa fyade sakamakon tashe-tashen hankulan da aka fuskanta a jihar, kama daga na kabilanci zuwa ‘yan ta’adda.
Yayin da a Jihohin Katsina da Kebbi da Sokoto da kuma Kaduna, yankunan da ke fama da matsalar ‘yan ta’adda da masu satar mutane, matan ke ci gaba da bayyana damuwar da suke ciki, kan matsalar fyaden da mata ke fuskanta.
Wani binciken da wasu dattawan arewacin Najeriya su ka yi, ya nuna cewa ƴaƴan da aka haifa sakamakon fyaɗe da masu garkuwa da mutane ke yi wa mata a yankunan Katsina zuwa Zamfara, sun kai dubu dari biyar a watan Agustan shekarar da ta gabata ta 2022, kamar yadda wani jigo a kungiyar Dakta Bashir Kurfi ya shaidawa BBC a kwanakin baya.
A nan Kano kuwa, majalisar dokokin jihar ce ta gbatar da kudirin doka da zai bai wa mata masu juna-biyu da kananan yara kulawa da lafiyarsu kyauta.
Wasu mata da muka zanta da su a nan Kano sun bayyana irin kalubalen da suka fuskanta a shekarar 2022 da ta gabata.
Shugabar kungiyar lauyoyi mata ta kasa da kasa FIDA reshen Jihar Kano Barista Bilkisu Ibrahim Sulaiman, ta ce babban abin da ke kara ta’azzara yawaitar aikata laifin fyade a cikin al’umma shi ne rashin samun zarafin gabatar da kwararan shaidu hujjoji daga wadanda aka yi wa fyaden.Shehu Abdullahi shi ne shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta kasa reshen Jihar Kano, ya yi Freedom Radio karin haske kan kididdigar da hukumar ta tattara a shekarar da ta gabata game da al’amuran da suka shafi take hakkin dan adam.
Dr Zahra’u Muhammad Umar ita ce kwamishiniyar harkokin mata ta Jihar Kano, ta ce gwamnatin jihar na bayar da fifiko a bangaren mata da kananan yara, musamman ma wadanda ke karkara.
Daga kasar Amurka kuwa, a cikin watan Afirilun bara ne dandazon mata da kananan yara ne suka gudanar da zanga-zangar neman hakkinsu, kan zargin nuna wariya da ake yi musu wajen daukar aiki.
Wannan dalili ne ya yi sanadiyyar mayar da hankalin mahukuntan kasar wajen kokarin daidaita daukar aiki tsakanin maza da mata a kasar.
Daga kasar Indiya kuwa, mata da kananan yara sun shiga rudani a shekarar da ta gabata, ta yadda aka rinka samun yawaitar aikata laifin fyade ga mata kanana har ma da manya, wanda ya sa a ko wace rana ake samun mata 50 da aka yi wa fyade a kasar.
Sai dai a karshen shekarar ta 2022 ne mahukuntan kasar suka bayyana raguwar faruwar yi wa matan da kananan yara fyade, da adadin ya koma kaso 40 cikin dari a ko wace rana.
Daga kasar China kuwa, wata kididdiga da aka fitar a shekarar da ta gabata, ta nuna cewa mata da kananan yara su ne kan gaba wajen yin rayuwa mai matukar wahala fiye da maza.
Inda a Brazil kuma rashin aikin yi ne ya yi wa mata katutu, biyo bayan rashin sanya su a cikin harkokin gudanarwar gwamnatin kasar, dalilin da ya sa suka gudanar da zanga-zangar lumana kenan har sau 20.
A nahiyar Afirka dai yawaitar aikata laifin fyade ga mata tare da danne hakkokinsu, baya ga sauran nau’o’i na tsangwama da suke fuskanta sun jefa su cikin halin kuncin rayuwa, wanda ya sanya tilasta musu barin gidajen iyayen su, tare da shiga wata rayuwar marar amfani da rashin tabbas.

 

Rahoton: Shamsiyya Faruk Bello

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!