Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta sha alwashin samar da aikin yi ga matasa a fannin kimiyya da fasaha

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin samar da ayyukan yi ga Matasa a fannin kirkire-kirkire da harkokin kimiyya da fasaha musamman ga mutanan dake da wata hikima ta musamman. 

Hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan sashin ayyuka na musamman ta ma’aikatar Yada labarai Hajiya Halima Ahmad Ishaq ta fitar, da ta ce gwamnati na kokarin  kawar da rashin aikin yi ga Matasa ta hanyar kirkirar wasu zauruka na musamman da za a rinka kirkirar ayyukan da matasa za su iya dogaro da kansu ta hanyar baje fasahar da kowa ke da ita. 

Hakan ya biyo bayan  wani taron tattaunawa na musamman na masu ruwa da tsaki kan harkokin kirkire kirkire da ya gudana a ma’aikatar kimiyya da fasaha ta Kano, wanda ofishin mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan ci gaban Ilimi Alhaji Habibu Hassan El-Yakub ya dauki nauyi. 

Da yake jawabi yayin taron tattaunawar Alhaji Habibu Hassan El-Yakub ya ce dole sai an fito da Matasan dake da  basirar kirkire-kirkire an tallafa musu za a iya kawar da rashin aikin yi a nan Kano.

Taron dai ya samu wakilci daga ma’aikatar Matasa da wasanni data Kasuwanci data Kere-kere da kuma kungiyoyi masu zaman kansu. 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!