Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta soke Makarantun ‘Yan Mari

Published

on

Biyo bayan karbar rahoton da kwamitin kwararru na sake duba yanayin karantun  Almajirai a jihar Kano wanda  Muhammad Tahar Adamu yake jagoranta  gwamnatin Kano ta bada umarnin soke makarantun ‘Yan Mari.

A cewar Muhammad Tahar Adamu “Baba Impossible” gwamnatin Jihar Kano ta soke ayyukan gudanar da duk wani gidan Mari a nan Kano, saboda irin ayyukan da suke gudanarwa.

Shugaban Kwamitin sake fasalta tsarinAlmajiranci a nan Kano Dr Muhanmad Tahar Adam ne ya sanar da hakan a yau lokacin da da ya jagoranci zagayen ziyarar gani da ido da jami’an hukumarsa ke gudanarwa a nan Kano, don tantance yadda ake gudanar da gidajen  ‘Yan Marin suke.

‘Yan mari 36 sun shaki iskar ‘yanci a Kano

Ko mene ne makomar ‘yan marin da ake sakowa?

Ganduje ya kaddamar da shirin makarantun Tsangayu da Al-qur’anai

Kazalika, Dr Muhammad Tahar Adam ya yi karin bayani kan cewa matakin bai shafi   Makarantun Islamiyya da na Allo ba.

Har ila yau, kwamitin yace ya gano cewar ana take hakkin yara a wasu daga cikin irin wadannan makarantu na ‘Yan Mari.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,764 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!