Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin kano ta umarci a gaggauta fitar da tsohon Sarki Aminu Ado daga gidan Nasarawa

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta umarci kwamishinan ƴan sanda da ya fitar da Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero daga gidan Sarki na Nasarawa cikin gaggawa domin zata fara aikin gyara a wannan lokacin.

Kwamishinan Shari’a na jiha Barista Haruna Isa Dederi ne ya bayyana hakan a daren Alhamis yayin taron manema labarai da ya gudanar a gidan gwamnati jihar.

Barista Haruna Isa Dederi yace gidan Sarki na na Nasarawa mallakin gwamnatin Jihar Kano ne don haka suka umarci kwamishinan Yan sanda
daya gaggauta fitar da tsohon sarkin.

Ya ƙara da cewa hukuncin da kotu tayi ya tabbatar da halaccin dokar da majalisar dokokin jihar Kano ta yi Wanda gwamna ya sawa hannu.

Kwamishinan Yace umarnin da kotu ta bayar ya halatta dukkanin wani hukunci da aka aiwatar Kafin umarnin da kotu ta bayar, inda ya Kara da cewa gwamnatin Jihar Kano ta dawo da Sarki Sunusi Kafin fitar waccen doka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!