Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta yaye dalibai daurarru  62 mazauna gidan Gyaran Hali

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta cigaba da tallafawa daurarrun da ke zaune a gidajen gyaran halin musamman basu ilimi mai nagarta dan bunkasa rayuwarsu.

Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne ya bayyana hakan a wajen yaye dalibai 62 dake zaune a gidan gyaran halin.

Alhaji Umar Faruk Ibrahim ya kara da cewa zasu ci gaba da saka idanu kan yadda ake koyar da daliban dake zaune a gidajen gyaran halin na jihar Kano.

Shugaban  da ke kula da gidajen gayran hali na jihar Kano Ado Inuwa ya ce  gwamnatin ta yi abunda ya dace sakamakon daukar nauyin karatun na su da ta yi har su ka kammala.

Shugaban  makarantar wacce aka kafa ta a gidan gyaran halin Kurmawa karkashin jagorancin DCC Mu’azu Tukur mai ritaya, ya ce  karatun hadin gwiwa ne da makarantar SAS da gidan makama da KERD duka karkashin ma’aikatar ilmin jihar.

Akalla dalibai 62 da biyu ne aka yaye maza da mata da ya samu wakilcin hukomomi daban-daban.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!