Labarai
Gwamnatin Kano ta yi alkawarin karasa ayyukan da ta fara cikin kankanin lokaci
Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin rubanya aiyyukan ci gaba da zasu bunkasa jihar ta fannin Ilimi, tattalin arziki, noma, kasuwanci, da lafiya domin ganin jihar ta hada kafada da sauran manyan jihohi na kasashen duniya da suka samu ci gaba.
Sakataren yada labaran gwamnan Kano, Abba Anwar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a fadar gwamnatin Jihar Kano.
Ya ce gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta samu lambar yabo ta jagoranci na gari da ci gaban al’umma da kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ke bayarwa ga gwamnatin da ta fi kowacce gudanar da aiyyukan raya kasa.
Abba Anwar ya kara da cewa, gwamnatin Kano ta karbi lambobin girma da dama ta fannin tsarin tafiyar da Ilimin Tsangayu da na Makarantun Allo bisa tsari dai-dai da Zamani, tare da tattabar da shirin bayar da ilimi kyauta.
Gwamnatin Kano zata sauya fasalin samar da gidaje
Gwamnatin Kano za ta fara karrama ma’aikatan lafiya
A cewar Sakataren yada labaran na gwamna Abdullahi Umar Ganduje a bangaren lafiya, jihar Kano ta yi zarra wajen yaki da zazzabin cizon sauro, inda jihar ta kashe sama da naira miliyan 500, wanda hakan ya sanya ta samu tallafi daga gidauniyar Duniya ta Global Fund, na kudi Billyan 11, don ci gaba da yaki da zazzabin na cizon sauro.
Wakilin mu na fadar gwamnatin Jihar Kano Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito cewa gwamnatin ta yi alkawarin karasa manyan ayyukan ci gaba da ta fara tare da fito da wasu sabbi.