Manyan Labarai
Gwamnatin Kano za ta fara karrama ma’aikatan lafiya
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya umarci kwamishinan lafiya na jhar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa da ya fara karrama jajirtattun ma’aikatan lafiya da suka nuna kwazo wajen gudanar da ayyukansu.
Gwamna Ganduje ya ce wannan tsarin zai karawa ma’aikatan lafiya kwazo tare da bunkasa harkokin kiyon lafiyar a jihar Kano.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin ne yayin bada takardar shaidar daukar aiki ga jami’an lafiya 920, inda ya ce Gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafawa tsarin lafiya da kuma inganta shi.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Gwamnan Abba Anwar ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kuma tabbatar da cewa, inganta tsarin lafiya a matakin farko na daga cikin abin da gwamnatin sa za ta fi baiwa fifiko, don samar da ingantaccijyar al’umma, musamman ma a yankunan karkara.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umarci sabbin ma aikata da su yi aiki tukuru da nuna kwarewa a wuraren da aka dauke su don bunkasa tsarin lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa, an dauki ma’aikata 626 karkashin hukumar kula da lafiya ta jiha, da kuma 294 karkashin hukumar kula da lafiya a matakin farko.