Labarai
Gwamnatin Kano ta yi wa ma’aikata 130 ƙarin girma

Gwamnatin Jihar Kano ta yi wa ma’aikatan ta su 130 ƙarin girma.
Wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan jama’a na Hukumar kula da harkokin ma’aikata Jamilu Mustapha Yakasai, ya fitar ce ta bayyana hakan.
A cewar sanarwar, yin karin girman ya biyo bayan cancantar da ma’aikatan suka yi.
Shugabar Hukumar, Hajiya Ladidi Ibrahim Garko, ta bayyana cewa daga cikin nauyin da ya rataya a wuyan hukumar akwai sanya ido da tabbatar da cewa ana bin dokoki da ka’idojin aikin gwamnati yadda ya kamata, tare da kira ga ma’aikata su kara jajircewa a ayyukansu.
Haka kuma, Kwamishina na Daya a Hukumar, Alhaji Abdullahi Mahmud Umar, da Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Sani Shehu Minjibir, sun jaddada muhimmancin aiki tukuru da bin ka’idoji yayin zaman da ya samu halartar mambobin kwamishin da daraktocin hukumar.
You must be logged in to post a comment Login