Labarai
Gwamnatin Kano ta yiwa ‘yan jaridu bita ta musamman
Mataimakin gwamnan jihar kano Kwamarat Aminu Abdulsalam Gwarzo ya bukaci yan jaridu da jami’an yada labarai da su rinka rungumar sauyin da ake samu a faggen yada labarai koda yaushe.
Mataimakin Gwamnan jihar kano kwamarad Aminu Abdul Salam Gwarzo ne ya bayyana hakan yayin bitar kwanaki shida da ma’aikatar yada labarai ta shirya ga jami’anta na kanan hukumomi 44 a jihar Kano.
Wanda ya ce ”cigaban da ake samu mai dauke da kalubale da yawa a aikin jarida ke kawo barazana ga ma’aikata, don haka nake kira ga duk wani jami’in yada labarai tun daga matakin farko a karatu zuwa makura, ko wadanda suka dauki tsawon shekaru a aikin, wajibi su yadda cewa fagen aikin yada labarai fage ne dake zuwa da sabon ilimi a Koda yaushe”.
Kwamred yace Akwai bukatar jami’an yada labarai su zama masu bibiya, karance-karance, shiga shafuka da kuma halartar bita don karawa juna sani domin su inganta aikinsu, jin ilimi ya ishi mutum ko gadara da dadewa cikin aikin zai iya sawa a bar mutum a baya .
Wasu daga cikin mahalarta bitar daga wasu kananan hukumomin sun bayyana gamsuwa da abubuwa da aka koya musu kan sha’anin yada labarai, tare da mika godiyarsu ga gwamnan jihar kano dama kwamishinan yada labarai daya jajirce wajen tabbatar da wannan bita.
A nasa bangaren kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya shaida cewa yanada yakinin jami’an da aka baiwa bita zasu kara inganta aikinsu don dama sun iya, sannan kashin farko ne suka kammala inda aka kawo kwararrun masu bada horo a fannoni daban – daban.
Dan tiye ya Kuma tabbatar da cewa za suyi kundi su mayar da duk takardun da aka gabatar Littafi domin ya zama tarihi ga mutane baya, don su ma su amfana .
kwamishina yace baya ga jami’an yada labaran, gwamnatin jihar kano zata shirya irini wannan bita ga masu bada rahoto na musamman da Gwamna ya dauka, da ma’aikatan radio na gwamnati da masu zaman kansu don kara inganta harkokin yada labarai a jihar kano.
A yayin biyar, kimanin jama’an yada labarai 214 ne rukunin farko suka rabauta da bitar daga ofisoshin yada labarai na kananan hukumomi 44, da ma’aikatar yada labarai baki daya, wanda Gwamnan Kano Eng. Abba Kabir Yusuf ya dauki nauyi.
You must be logged in to post a comment Login