Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nasarorin hukumar NAHCON daga 2020-2023

Published

on

Ƙungiyar yaɗa harkokin addinin Muslinci ta ƙasa ta yaba da irin kokarin da shugaban hukumar kula aikin hajji ta ƙasa NAHCON mai barin gado Zikrullah Hassan Kunne ya yi na bunƙasa harkokin aikin hajji musamman a zamanin annobar corona.

Shugaban kungiyar na ƙasa Injiniya Kamal Olalekan ya yaba da kokarin nasa cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’an hulda da jama’a na kungiyar Alhaji Mu’ideen Adeleke

Injiniya Kamal Olalekan ya ce, gabanin kammala shugabancin Zikrullah Kunle Hassan a hukumar NAHCON ya yi kokari na ganin alhzan Najeriya sun sauke farali a 2022 lokacin da kasar Saudiyya ta dauki matakin rage yawan Alhazan da za su shiga kasar daga Najeriya zuwa dubu arba’in da biyar maimakon dubu casa’in da biyar na kujerun da ta saba bawa Najeriya a baya.

Sai dai duk da haka alhzan kasar nan sun sauke farali kasancewar Saudiya ta sanar da gudanar da aikin Hajjin a kurarren lokaci amma hakan bai hana Hukumar NAHCON karkashin jagorancin Barista Zikrullah Kulle Hassan yi musu shirin da ya kamata ba.

Wannan na zuwa ne bayan da ya kama aiki a shekarar 2020 da 2021 lokacin da duniya ke fama da matsin tattalin arziki da kuma annobar corona da ta tilasta hana shige da fice tsakanin kasashe ciki har da Saudiyya, wanda hakan ya bashi damar samar da tsare tsare tafiyar da harkokin aikin hajji cikin nasara, duk da a shafe tsawon shekara biyu ba a gudanar da aikin hajjin ba.

Kungiyar ta kuma ce, ta lura da irin namijin kokarin da Zikirullah Kunle ya nuna a aikin Hajjin 2023 bayan da kasar Saudiya cire dokar korona baki daya sannan ta mayarwa Najeriya adadin yawan kujerun aikin Hajjin zuwa dubu 95 kamar yadda ta saba a baya.

A cewar injiniya Kamal matakin da NAHCON ta dauka na tabbatar da ganin duk wani maniyyaci da ya biya kudin kujerarar aikin Hajji a shekarar da ba a yi aikin ba ya samu tafiya batare da barin ko guda ba, baya ga neman izinin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ya sahalewa NAHCON ta kara yawan Jiragen dake jigilar Alhazan Najeriya zuwa biyar kuma ya amince da hakan.

Kungiyar ta ce, a zamanin Zikrullah Hassan ya yi kokari wajen kara yawan Jami’an lafiya kwararru msu kula da lafiyar Alhazan tare da tabbar da ganin kashi casa’in da biyar cikin dari na alhazan sun fara ziyara Madina kafin zuwansu Makka, duk da rikicin Sudan da ya hana Binta saman kasar.

Gabanin barinsa kujerar NAHCON Zikrullah Kunle ya kafa Kwalejin Nazarin harkokin akin Hajji baya ga bunkasa shirin tara kudin zuwa aikin Hajji a da ake kira adashin gata ya kuma kara samarwa Hukumar hanyoyin kara samun kudaden shiga, baya ga kokarin da yake yi kafin cikar wa’adin da na dawo da harkokin ciyar da alhazai zuwa kasar nan.

Barista Zikrullah Kulle Hassan ya kama aiki a shekarar 2020 ne adaidai lokacin da duniya fama da matsar tattalin arziki sakamakon cutar Corona ya kuma yi ƙoƙari wajen mayar da aikace aikacen hukumar da harkokin aikin Hajj da Umara zuwa na zamani, ya kuma kara yawan ofisoshin NAHCON na shiyya -shiyya domin samun saukin gudanar da aikinta.

Kulle Hassan, ya kuma mayar da hankali wajen ganin ma’aitansa na samun ƙarin ilimi a kan aikinsu ta hanyar ba su horo ya kuma gina Asibiti da masallacin Juma’a a harabar hukumar.

Duk da tarin kalubalen da ya fuskanta ba su sanya gwiwar Zikrullah ta yi sanyi wajen samar da cigaban NAHCON ba

“Kulle Hassan, ya gudanar da shugabancinsa cikin mutunta kowa batare dagawa ko nuna banbanciba ya kuma bawa kowa damarsa ta guidance da aikin tare da bude Kofa domin karbar shawara daga masu ruwa da tsaki da kuma sauran ma’aikatansa, sannan ya samu kyakkyawwn yabo wajen aiki da kwamishinoninsa a tare cikin girmama juna”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!