Labarai
Gwamnatin Kano za ta gabatar da kasafin kudi mafi yawa a tarihin jihar

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zai gabatar da kasafin kudin jihar na shekarar 2026 da ya kai naira tiriliyan ɗaya mafi yawa a tarihin jihar.
Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin wani zama na musamman kan kasafin kuɗin 2026.
Sanarwar ta ce a mako mai zuwa ne ake sa ran gwamnan zai gabatar da kasafin a gaban majalisar dokokin jihar domin yin muhawara a kai.
Wannan ne karo na farko da jihar za ta kashe kuɗi mafiya yawa a kasafin kudin ƙasar.
Gwamnan Abba Kabir ya kuma danganta ƙaruwar kuɗin kasafin da yadda aka samu bunƙasar hanyoyin tara kuɗin shigar jihar a cikin gida.
Abba Kabir ya ce kasafin kuɗin wannan shekara zai mayar da hankali kan noma da ilimi da kiwon lafiya tare da ƙarfafa matsakaita da ƙananan sana’o’i.
You must be logged in to post a comment Login