Kasuwanci
Gwamnatin Kano za ta karrama ƴan kwangilar da suka yi aiki mai inganci- Nura Ma’aji

Gwamnatin jihar Kano za ta karrama ‘yan kwangilar da ta tabbatar da aiyyukan su na da inganci kuma sun gudanar da su yadda ya kamata.
Kwamishinan ma’aikatar lura bibiya da duba ingancin aiyyuka na jihar Kano, Kwamred Nura Iro Ma’aji Sumaila ne ya bayyana hakan, ya yin ziyarar duba wasu aiyyuka da gwamnatin jiha ke aiwatar wa.
Nura Iro Ma’aji, ya yaba da aikin da wani kamfani yake gudanarwa a kwalejojin Fasaha na GTC Ungoggo da Dambatta, da ya ce gwamnatin jiha zata karrama ire-iren su nan ba da dadewa ba a dakin taro na Coronation hall dake gidan gwamnatin Kano.
A nasa jawabin shugaban karamar hukumar Dambatta Jamilu Abubakar, ya yaba wa kwamishinan da kuma ma’aikatarsa bisa yadda suke bibiyar aiyyukan yadda ya kamata.
A ziyarar tantance aiyyukan, tawagar ta duba aikin zuba Kwaltar hanyar Sabo Bakin Zuwo, sai gyare -gyare na Dakin kwanan Dalibai Mata a makarantar koyon aikin Unguwar Zoma da titunan Kilomita 5 na Kananan hukumomin Makoda sai Ghari da Tsanyawa.
You must be logged in to post a comment Login