Labarai
Gwamnatin Kano za ta kashe fiye da Biliyan 15 wajen biyan bashin tsoffin Kansiloli

Majalisar Zartaswa ta Jihar Kano, ta amince da kashe kimanin Naira biliyan 15 da Miliyan 667 da dubu dari 634 da naira 645 da kwabo 10 domin biyan kudin sallama da alawus na tsoffin kansiloli daga shekarar 2014 zuwa 2024.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Talata.
Wayya, ya kara da cewa, Majalisar zartaswa ta Kano, ta amince ne da kashe kudade har Naira 51 da miliyan 575 da dubu 700 da Naira 575 da Kwabo 96 ne yayin zaman da ta gudanar a ranar 27 ga watannan da muke ciki na Afrilu, karkashin jagorancin Gwamnan Injiniya Abba Kabir Yusif inda a cikin kunshin kudaden ne za a sallami tsoffin kansilolin.
You must be logged in to post a comment Login