Labarai
Gwamnatin Kwara ta musanta mutuwar ɗan NYSC sakamakon zazzbin Lassa

Gwamnatin Jihar Kwara ta musanta rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa wani ɗan bautar ƙasa ya rasa ransa sakamakon kamuwa da zazzbin Lassa, a sansanin horas da matasa masu bautawa kasa na jihar.
Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren yada labarai na ma’aikatar lafiyar jihar Saad Hamdalat, bayan da ma’aikatar ta gudanar da binciken gaggawa.
Sanarwar ta ce, sakamakon binciken karkashin kwararriyar Likita Dr Khadeejah Kamaldeen, bai bayyana wata shaida ta samuwa ko yaduwar zazzabin Lassa a sansanin NYSC din ba.
Haka kuma ba a samu wani ko wata da ake zargi da cutar ba, sai dai an ƙara tsaurara matakan kariya ga yan bautar kasar a sansanin.
You must be logged in to post a comment Login