Connect with us

Labarai

Gwamnatin mu na ɗaukar tsauraran matakai don shawo kan matsalar tsaro- Shettima

Published

on

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ɗaukar tsauraran matakai  domin shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar Najeriya.

 

Ya ce, gwamnatin su  ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin sassan Najeriya.

 

Ta cikin wani sako Shettima ya ƙara da cewa, sabbin tsare-tsare da dabarun tsaro da gwamnati ke aiwatarwa sun haɗa da ƙarfafa rundunonin tsaro, inganta kayan aiki, da kuma haɗin gwiwa da ƙasashen waje domin yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka.

 

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma jaddada cewa, duk da ƙalubalen da ake fuskanta, gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaro gaba ɗaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!