Connect with us

Labarai

Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da zargin Amurka

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da rahoton wasu ‘yan Majalisar Dokokin Amurka da suka zargi Najeriya da nuna wariya ta addini, tana mai cewa babu wata manufar gwamnati da ke goyon bayan tsananta wa kowace ƙungiyar addini. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana haka yayin martani kan rahoton da aka miƙa wa Shugaba Donald Trump.

 

Rahoton ya biyo bayan binciken da kwamitocin Majalisar Wakilai ta Amurka suka gudanar kan zargin tsananta wa Kiristoci da matsalolin tsaro a Najeriya. Sai dai Gwamnatin Tarayya ta ce matsalolin tsaro da suka haɗa da ta’addanci, fashi da makami da rikice-rikicen ƙabilanci ba su da alaƙa da wata manufar wariyar addini.

 

Gwamnatin ta jaddada cewa kundin tsarin mulki ya tabbatar da ‘yancin addini ga kowa da kowa, tare da ƙara da cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, tare da bunƙasa dangantaka mai kyau da Amurka ta hanyar diflomasiyya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!