Manyan Labarai
Gwamnatin Najeriya zata dauki masu kwarewa a fannin koyarwa
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta dauki dukkannin wadanda suke da kwarewa a bangaren koyarwa musamman wadanda suka samu takardar shaidar malanta kamar yadda ma’aikatar ilimi ta bukata.
Babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta Najeriya Sonny Echono ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke duba yadda jarabawar neman kwarewa a bangaren koyarwa da cibiyar rajistar malamai ta kasa TRCN ta shirya a Abuja.
Ya ce, wannan mataki yana daya daga cikin yunkurin da gwamnati ke yi wajen ganin an kakkabe baragurbin malamai daga makarantun kasar nan.
A cewar sa, gwamnatin Najeriya da gaske ta ke ba gudu ba ja da baya kan yunkurinta na sallamar malaman da basu da kwarewar aiki, matukar wa’adin da ta sanya ya cika.
Babban sakatare a ma’aikatar ilimi ta Najetiya ya kuma ce, mataki na gaba da za su dauka bayan samar da kwararrun malamai a makarantu shine kafa hukumar da za ta rika kula da makarantun Sakandire wanda kuma a cewar sa tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da hakan.