Kasuwanci
Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da sabbin jiragen Ruwa da Riguna
Gwamnan Jihar Sokoto, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da sabbin jiragen ruwa na zamani guda ashirin tare da rigunan ruwa guda dubu biyu, domin rage haɗurran da ake fuskanta sakamakon ambaliya da kuma nutsewar jirage a sassan jihar.
Bikin ƙaddamarwar ya gudana ne a tashar ruwa da ke cikin birnin Sakkwato, inda gwamnan ya bayyana cewa, wannan mataki wani ɓangare ne na manufofin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ce duk shekara jama’a da dama na rasa rayukansu, musamman a ƙauyukan da ke bakin kogin da sauran manyan ruwan jihar, lamarin da ya sa gwamnatin ta samar da wadannan jirage da rigunan ruwa domin inganta sufuri da rage haɗurra.
A nasa jawabin, kwamishinan harkokin sufuri na jihar ya gode wa gwamnan bisa wannan muhimmiyar gudummawa, yana mai cewa tun kafuwar jihar ba a taba samun irin wannan kayan a lokaci guda ba.
Haka kuma, wasu daga cikin wakilan al’umma daga yankunan bakin ruwa sun bayyana farin cikinsu da jin daɗin wannan shiri, inda suka ce hakan zai rage tsoron da suke fuskanta a duk lokacin tafiya musamman a damina.
You must be logged in to post a comment Login