Labarai
Gwamnatin Sokoto ta raba kayan abinci da miliyan 293 ga ƴan gudun Hijira da mutanen da harin ƴan bindiga ya shafa

Gwamnatin Jihar Sokoto ta raba wa mutanen da hare-haren ƴan bindiga suka rutsa da su da kuma ’yan gudun hijira kayan tallafi da suka hada da Naira miliyan 293 da buhunan abinci guda 2,540.
Gwamna Ahmed Aliyu ne ya sanar da hakan a wata ziyarar jajantawa jama’ar da abin ya shafa a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni, inda ya mika kudi da kayan abinci ga iyalan da suka rasa ’yan uwansu, wadanda suka jikkata, da kuma ’yan gudun hijira.
A karamar hukumar Isa, gwamnan ya bai wa iyalan wadanda suka mutu kudi Naira miliyan biyu da buhunan shinkafa guda biyar ga kowane iyali daga cikin iyalai 65 da abin ya shafa.
Haka kuma, wadanda suka jikkata mutum biyar sun samu Naira dubu dari biyu da hamsin da kuma buhunan shinkafa uku kowannensu.
Baya ga haka, gwamnan ya raba Naira miliyan ashirin da buhunan abinci 1,200 ga ’yan gudun hijira a yankin, wanda gaba ɗaya ya kai tallafin da ya baiwa al’ummar Isa Naira miliyan 151 tare da buhunan abinci 1,240.
You must be logged in to post a comment Login