Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da jimawa ba zata dawo da batun Najeriya air

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da dadewa ba za ta dawo kan batun kafa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasa wato Nigeria Air.

 

Karamin ministan sifirin jiragen sama na kasa Sanata Hadi Sirika ne ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kunshin kasafin kudin ma’aikatar sa gaban kwamitin kula da harkokin jiragen sama na majalisar dattawa.

 

A cewar Sanata Hadi Sirika, dama tun farko an dakatar da shirin ne na wucin gadi domin sake shiri, yana mai cewa nan gaba ba da dadewa ba al’ummar kasar nan za su fara cin gajiyar kamfanin na Nigeria Air.

 

Ministan ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari tun  bayan darewar sa karagar mulki a shekarar dubu biyu da goma sha biyar, ya nuna damuwar sa kan yadda duk da cewa kasar nan ke da kasuwan siifirin jiragen sama amma kuma babu wani kamfani na kasar nan da ya ke cin gajiyar lamarin.

 

Sanata Hadi Sirika ya kuma ce kamar dai yadda aka tsara tun da fari bangarorin masu zaman kansu ne za su samo da kaso mafi yawa na kudaden da za a kashe wajen gudanar da shirin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,746 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!