Connect with us

Kiwon Lafiya

Boko haram:sun kai hari kauyukan da kan iyakan jihohin Adamawa da Borno a jiya

Published

on

Dagacin Duhu na jihar Adamwa Mohammed Sanusi ya ce mayakan  kungiyar Boko Haram sun kai hari kauyukan da ke kan iyakokin jihohin Adamawa da Borno da ya hada da Michika da Madagali a daren ranar Litinin da ya sanaya sukan kona gidaje saboda su yi jidon kayayyakin abinci ne.

Wasu mazauna yankin da suka boya da wanda suke tsire kan tsaunika sun shedawa manema labarai cewa a yayin kai harin ‘ya’yan kungiyar Boko Haram sun yi wa yara kanana da datijawa da kuma barasa lafiya da bindigogi.

Sai dai kawo yanzu hukumomin tsaro ba su bayyana irin asarar da aka tafka ba.

A cewar Malam Sanusi ya ce ‘yan tada kayar bayar sun dawo kauyukan ne domin daukar fansa, bayan da suka gaza yin katabus yayin kai harin da suka yi na karshe a yankunan Michika da Madagali kwanaki 7 ke nan, kasancewar rundunar sojan saman kasar nan ta maida martani.

Rahotanni sun bayyana cewar wannan shi ne hari na 3 da kungiyar Boko Haram din da kai wadannan kauyuka na Madagali da Michika a jihar Adamawa a cikin wata guda

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!