Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta ce rundunar soja ta ci galabar kwato mutane dubu uku da kungiyar boko haram ta kama

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce kimanin mutane dubu 30 da yan kungiyar Boko Haram suka sace ne Rundunar sojin kasar nan tayi nasarar kubutar wa.

Ministan tsaron kasar nan Birgediya Janar Mansur Dan Ali mai ritaya ne ya bayyana Hakan yau a garin Maiduguri a wani taron jin ra’ayin jama’a da aka shiryawa jami’an soji da sauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin tarayya bazata yi kasa a gwiwa ba wajen kakkabe sauran yan kungiyar Boko Haram da suka rage a fadin kasar nan tare da tabbatar da zaman lafiya.

Da ya ke jawabi a yayin taron ministan cikin gida Laftanar janar Abdulrahman Dambazu mai Ritaya ya ce rundunar sojin kasar nan ta riga ta gama ruguje kungiyar Boko Haram tare da duk wani abu da ya shafe ta.

Shima a nasa bangaren Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammadu ya bayyana cewa dawowar tashi da saukar jiragen sama wasanni da sauran al’amura ya jihar na alamta cewa a jihar ta samu zaman lafiya na dawo wa jihar ta Borno.

A ta bakin gwamnan jihar ta Borno Alhaji Kashim Shettima yabawa rundunar sojin kasar nan yayi kan irin kokarin da suke yi wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 341,026 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!