Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta ce zata rage kudin ruwa da kamfanonin sarrafa shinkafa ke biya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce za ta rage kudin ruwa da masu kamfanonin sarrafa shinkafa su ke biya a bashin da suke karba daga gareta.

 

Shugaban kwamitin karta kwana da shugaban kasa ya kafa domin farfado da noman shinkafa a kasar nan Alhaji Atiku Bagudu ne ya bayyana haka ya yin wani taron masu ruwa da tsaki kan noman shinkafa jiya a Lagos.

 

Alhaji Atiku Bagudu wanda shi ne gwamnan jihar Kebbi, ya ce ba ko shakka gwamnati za ta duba bukatar masu kamfanonin shinkafar wanda suka bukaci neman rage musu kudin ruwa da su ke biya a rancen da suke karba daga bankuna.

 

Ya ce gwamnati na namijin kokari domin tabbatar da cewa al’ummar kasar nan sun dogara da kansu wajen samar da shinkafa da zai biya bukatun su na yau da kullum.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!